Chelsea ta tuntubi tsohon kocin Paris Saint-Germain Mauricio Pochettino a kwanakin baya kan yiwuwar ya maye gurbin kocin rikon kwarya Frank Lampard a Stamford Bridge.
An bayyana hakan ne ta hanun, Romano Fabrizio, a cikin wani sakon twitter ta shafinsa na Twitter ranar Alhamis.
“Chelsea kuma ta tuntubi Mauricio Pochettino a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata. Wannan ita ce hanya ta farko kai tsaye bayan bazarar da ta gabata lokacin da yake cikin jerin, ”Romano ya wallafa a shafinsa na Twitter.
“Babu wani abu da ya ci gaba tukuna, Nagelsmann ya kasance mafi fifiko. Za a ci gaba da tattaunawa, domin Chelsea na son tabbatar da kaso 100% na zabin da za ta yi.”
Har yanzu Chelsea na neman koci na dindindin wanda zai maye gurbin Lampard a bazara.
Kwanan nan Blues ta kori Graham Potter kuma ta nada Lampard na dan lokaci don ya jagoranci kungiyar ta farko har zuwa karshen kakar wasa ta bana.


