Dan wasan gaba na Chelsea, Pierre-Emerick Aubameyang, na iya ganin an kawo karshen kwantiraginsa da kungiyar a wannan bazarar.
Kungiyar ta Premier ta fusata bayan tafiyar Aubameyang na baya-bayan nan don tallafa wa tsohuwar kungiyarsa Barcelona da Real Madrid a wasan El-Clasico na karshen makon da ya gabata.
Kodayake kwantiraginsa zai kare a watan Yuni 2024, da alama Blues na iya kokarin sauke shi kafin lokacin.
Karanta Wannan:Â Guinea ta fara shirye-shryen tunkarar Najeriya
Inter Milan na duba yiwuwar siyan Aubameyang.
Kungiyar kwallon kafa ta Seria A dai na neman kara kaimi wajen kai hari, inda Romelu Lukaku zai koma Chelsea idan yarjejeniyar aro ta shekara daya ta kare.
A cewar La Gazzetta dello Sport, dan wasan na Gabon yana daya daga cikin ‘yan wasan da Inter ke nema kafin kakar wasa mai zuwa.
Aubameyang ya fara aikinsa a abokan hamayyar Inter AC Milan, ko da yake bai buga musu gasa ba.