Rahotanni sun bayyana cewa, Chelsea ta bi sahun Real Madrid da Liverpool wajen zawarcin dan wasan Paris Saint-Germain Kylian Mbappe.
A cewar Daily Record, PSG ta karfafa yunƙurin da Chelsea ke yi don tabbatar da sa hannun Mbappe bayan tattaunawa kai tsaye da mai haɗin gwiwar Blues Todd Boehly kan yuwuwar canja wurin dan wasan gaba.
Chelsea, karkashin jagorancin Boehly, tana ƙoƙarin yin shawarwari kan yarjejeniyar ‘yan wasa da kuɗi don kawo ɗan wasan Faransa zuwa Stamford Bridge a wannan bazarar.
A halin yanzu ba a san makomar Mbappe a PSG ba saboda har yanzu bai rattaba hannu kan sabon kwantiragi da Parisians ba.
Kwantiraginsa da zakarun gasar Ligue 1 ta Faransa za ta kare a bazara mai zuwa.
An sanya Mbappe akan kudi Yuro miliyan 250 kwatankwacin (£214m).