Gwamnatin kasar Chadi ta fitar da wani shiri na samar da ƙarin ruwan sha da na wutar lantarki ga gidaje har zuwa karshen shekara.
A karkashin wannan yunƙurin, gidaje za su sami ruwan sha da wutar lantarki kyauta a kowane wata.
Bugu da kari, gwamnatin ƙasar ta yi alkawarin biyan bashin kudaden ruwa da na wutar lantarki da ke kan mazauna yankin.
A wani yunkuri na rage radadin kudi, gwamnatin ta kuma sanar da rage harajin sufuri, wanda zai iya rage kudaden da ake kashewa wajen sufuri.
Wannan shawarar ta zo ne a matsayin martani ga hauhawar farashin man fetur a baya-bayan nan, wanda ya haifar da ƙarin farashin sufuri. In ji BBC.
Manufar, wacce shugaban mulkin sojan Chadi kuma shugaban rikon kwarya Mahamat Deby ya amince da shi, na da nufin tallafa wa gidaje a lokutan wahala.
Sai dai wasu ‘yan kasar Chadi na kallon wannan mataki a matsayin dabarun siyasa na samun goyon bayan masu kaɗa kuri’a, yayin da Mahamat Deby ke shirin tsayawa takarar shugabancin ƙasar a zaɓukan dake tafe tsakanin watan Mayu da Yungamnatin kasar ta yi, har yanzu akwai rashin gamsuwa a tsakanin mazauna yankin, musamman a yankunan kamar babban birnin kasar, N’Djamena, inda aka shafe makonni biyu ana ɗauke wutar lantarki.
Sai dai kuma, ‘yan kasar Chadi da dama na maraba da shirin a matsayin agajin da ake bukata a cikin mawuyacin halin da ake ciki na tsadar rayuwa.


