Ƙasar Chadi ta ce ta kira jakadanta a Isra’ila zuwa gida don tattaunawa game da “hare-hare da tashin hankalin da ba a taɓa gani ba a Zirin Gaza”.
Cikin wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, gwamnati ta yi tir da “rasa rayukan fararen hula kuma ta yi kira a tsagaita wutar da za ta kai ga samun kwanciyar hankali ga Falasɗinawa”.
A shekarar 1972, Chadi wadda Musulmai suka fi rinjaye, ta yanke hulɗar da jakadanci tsakaninta da Isra’ila, har sai a 2019 suka daidaita.
Yanzu Chadi ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta ɗauki irin wannan mataki tun bayan fara yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba.
Zuwa yanzu, ƙasashen Turkiyya, da Chile, da Bahrain, da Honduras, da Colombia, da Jordan sun janye jakadunsu daga Isra’ila don nuna ɓacin ransu da hare-haren na Isra’ila a Gaza.
Isra’ila ta ce mayaƙan Hamas sun kashe mutum 1,400 lokacin da suka kai hari ranar 7 ga Oktoba, inda ta ci alwashin ganin bayan ƙungiyar a hare-haren ramuwar gayya – waɗanda suka kashe Falasɗinawa sama da 9,500 zuwa yanzu.