Babban bankin ƙasa, CBN, na shirin sakin duk wasu takardun kudi na N1,000, N500, da N200 ga bankunan.
A cewarsa, babban bankin ya kammala shirin raba tsofaffin takardun kudi ga bankunan Deposit Money a fadin kasar nan daga ranar Alhamis (yau).
Ya kara da cewa wannan ci gaban zai kawo karshen karancin Naira da aka shafe watanni biyu ana fama da shi a Najeriya.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta shirya yajin aiki da zanga-zanga a ma’aikatun CBN a fadin kasar biyo bayan wahalhalun da manufofin bankin na sake fasalin naira suka haifar.
Sabon hukuncin na CBN ya zo ne makonni da yawa bayan da Kotun Koli ta ba da umarnin cewa tsofaffin takardun kudi na N1,000, N500 da N200 su ci gaba da kasancewa a kan doka har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.