Babban bankin ƙasa CBN, ya kaddamar da wani shirin musayar kudi a kananan hukumomin kasar nan 774, a wani bangare na aiwatar da manufofin sake fasalin kudin Naira.
Shirin tsakanin CBN, Deposits Money Banks, DMBs, da Super Agents zai fara aiki ne a ranar 23 ga Janairu, 2023, don musanya sabbin takardun kudi na Naira da tsoffin takardun kudi.
CBN ya dage a ranar 31 ga watan Junairu, 2023, wa’adin tsaffin takardun kudi na Naira zai daina aiki.
Sanarwar na ƙunshe ne a wata takardar hadin gwiwa a ranar Juma’a mai dauke da sa hannun daraktan sashen kula da harkokin bankuna na CBN, Haruna Mustafa, da daraktan sashen tsarin biyan kudi, Musa Jimoh.
Ya bayyana cewa, musayar kuɗi za ta kasance mafi girman 10,000 ga kowane mutum.
“Za a iya musanya tsofaffin takardun kudi na N1000, N500, da N200 don sabbin takardun kudi da aka sake tsarawa da/ko na kasa da ake da su (N100, N50 da N20, da dai sauransu), wadanda suka ci gaba da zama doka.
“Wakili zai canza mafi girman N10,000 ga kowane mutum. Adadin da ya haura N10,000 ana iya ɗaukar su azaman ajiya a cikin wallet ko asusun banki daidai da tsarin tsabar kuɗi. Ya kamata a kama bayanan abokin ciniki na BVN, NIN, ko bayanan katin cirar kuɗi gwargwadon iko.”


