Babban bankin ƙasa (CBN), ya zargi wasu bankunan kasuwanci a Fatakwal na jihar Ribas da kin amincewa da fitar da makudan kudade da aka sake fasalin na Naira biliyan 4.5 da aka ware musu.
Shugaban bankin na CBN reshen jihar Ribas, Maxwell Okafor ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a lokacin da ya jagoranci tawagar jami’an tsaro kan sabbin takardun kudi da aka yi wa kwaskwarima ga wasu bankunan kasuwanci da kasuwanni a Fatakwal.
Okafor ya bayyana cewa, CBN ya raba kusan Naira biliyan 4.5 na sabbin takardun kudi na Naira ga bankunan kasuwanci a jihar tsakanin ranakun Alhamis zuwa Juma’a, inda ya yi mamakin dalilin da ya sa yawancin kwastomomi ba sa samun su.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda wasu bankunan jihar ke dakile yunkurin da CBN ke yi na ganin an aiwatar da kashe sabbin kudaden Naira ta hanyar ajiye su a asusun ajiyar su na banki.
“Muna sa ido kan yadda ake raba sabuwar takardar kudin Naira, kuma tunanin da muka samu ba abin karfafa gwiwa ba ne. Mun ziyarci wasu bankuna, kuma daya daga cikinsu ba ya fitar da sabbin takardun Naira,” inji shi.


