Babban bankin ƙasa CBN, ya umarci bankuna da su yi aiki a yau Asabar da kuma gobe Lahadi, domin tabbatar da cewa takardun kuɗaɗen naira sun wadata a hannun jama’a.
A wata sanarwa da CBN ya wallafa a shafin na Tuwita, ya ce, ya fito da maƙudan takardun naira ne a bankuna da kuma na’urorin cirar kudi ta ATM domin magance matsalar ƙarancin kuɗin da ake fama da shi a fadin ƙasar nan.
Sanarwar ta ƙara da cewa CBN ya bayar da umarnin ɗaukar takardun kuɗaden daga rassansa zuwa bankunan kasuwanci da ke fadin ƙasar nan.
Ta ƙara da cewa bankunan kasuwanci sun samu maƙudan takardun kuɗaɗe domin rarraba wa abokan huldarsu, da nufin wadatar kuɗade a hannun jama’a.
Sanarwar ta ci gaba da cewa babban bankin ya umarci bankunan kaswunci da su sanya takardun kuɗaɗen cikin na’urorin cirar kudinsu na ATM, domin sauƙaƙa wa kwastomominsu.