Babban bankin ƙasa CBN, ya kwantar da hankula mutane kan fargabar da ake nunawa na karuwar farashin dala da ke sake durkusar da Naira, yana cewa, zai yi kokari domin ganin an samu sassauci.
Wannan na zuwa ne bayan bankin ya gargadi masu yaɗa jita-jita a kasuwanni bayan fagge.
A lokacin da ya ke tsokaci kan karuwar farashin dala wanda tuni ake ganin tasirin haka a wajen ciniki da sauran kasuwanci, Daraktan harkokin yada labarai, Mista Osita Nwanisobi, ya ce, bankin ya durƙufa wajen ganin ya shawo kan manyan ƙalubalen da kasuwar canji ke fuskanta, da kuma ganin an kawo sauki.
CBN ya ce, babu shaka ana fama da ƙarancin dala musamman a wannan lokaci da bukatar dalar ke karuwa ga manya kamfanoni da masu biyan kudin makaranta da kiwon lafiya da dai saransu.
Sai dai ya ce, bankin a yanzu damuwarsa shi ne darajar Naira, da kuma ganin yada za a taimaki Najeriya wajen daidaita kuɗinta da kuma matsalolin da ake samu ta fanin cinikin mai.
A makon da ya gabata sai dai kungiyar masu canjin kudin kasashen waje ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta dauki matakan dakatar da faduwar da darajar takardar kudin kasar ke cigaba da yi a kan dalar Amurka.
Kungiyar ta ce a cikin makon farashin dalar ya karu da kusan Naira 100, abin da ba a taba gani ba a tarihi