Babban Bankin Najeriya CBN ya musanta rahotonnin da ke cewa gwamnan bankin Godwin Emefiele ya alaƙanta rashin wadatattun takardun buga sababbin kuɗi a ƙasa, kan ƙarancin takardun buga kuɗin.
Jaridar PREMIUM TIMES a ƙasar ce dai ta ruwaito wata majiya na shaida mata cewa Godwin Emefiele ya bayyana wa taron majalisar magabatan ƙasar cewa rashin isassun takardun buga kuɗi ne ya haddasa ƙarancin takardun sababbin kuɗin a ƙasar.
To amma a wata sanarwa da CBN ɗin ya fitar ya ce, babu inda gwamnan banki ya faɗi haka a lokacin da yake yi wa majalisar magabatan jawabi ranar Juma’a a fadar shugaban ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa abin da Mista Emefiele ya faɗa wa majalisar shi ne hukumar da ke lura da buga kuɗin na aikin buga kuɗin domin wadata ‘yan ƙasar da takardun kuɗin da suke buƙata domin harkokinsu na yau-da-kullum.
”Hukumar da ke Lura da Buga Kuɗi ta Ƙasa tana da isassun kayan aikin da take buƙata wajen buga sabbin kuɗin da za su wadatar. Dan haka CBN ke kira ga jama’a da su yi watsi da rahotonnin da ke cewa babu isassun takardun buga kuɗin tare da kiran jama’a su ƙara haƙuri, kasancewar muna bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun ƙara yawan kuɗin da ke yawo a hannun mutane”, in ji sanarwar.
Haka kuma sanarwar ta ce akwai wani sautin murya da ke yawo a shafukan sada zumunta wanda ke zargin cewa CBN na shirin rufe wasu bankuna, musamman a wasu yankunan.
Dan haka sanarwar ta ce CBN ba shi da wannan shiri, kuma saƙon da ke cikin muryar ya saɓa wa dokar tsarin banki na ƙasar.
Dan haka CBN ɗin ya shawarci ‘yan ƙasar da su yi watsi da saƙon sautin muryar kasancewar ba daga bankin yake ba.