Babban bankin kasa CBN, ya sanar da sayar da dala ga ƴan canji.
Babban bankin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na intanet ranar Litinin.
Babban bankin ya ce ya shirya sayar da dala 10,000 ga kowanne kamfanin canji a kan N1101.
Ya kuma umarci ƴan canjin da su sayar da dala kan karin da bai wuce kashi 1.5 cikin 100 kan farashin na CBN.
Faɗuwar da darajar nairar ta dinga yi a makonnin da suka wuce ta jawo ɗaukar matakai daban-daban daga ɓangaren hukumomi ciki har da kama ‘yan kasuwar canjin da jami’an tsaro suka yi a manyan birane kamar Kano, da Abuja, da Legas.