Babban bankin Najeriya, CBN, ya umarci cibiyoyin hada-hadar kudi wato bankuna, da su rika amfani da kafafen sada zumunta na abokan hulda domin tantancewa.
Babban bankin ya kuma bukaci cibiyoyin hada-hadar kudi da su sami adiresoshin imel, lambobin waya, da adiresoshin wurin zama, da dai sauransu, daga abokan ciniki.
Umurnin dai na kunshe ne a cikin sabbin ka’idojin tantance kwastomomi na CBN, wadanda ta ce suna da nufin karfafa tsarin tantancewa a tsarin banki.
An buga daftarin doka na CBN (Customer Due Diligence) na 2023 a shafinsa na yanar gizo ranar Juma’a.
A cewar CBN, an tsara wannan sabuwar dokar ne, domin samar da karin matakan tantance kwastomomi ga cibiyoyin hada-hadar kudi a karkashin tsarin sa.
Yayin da yake bayyana makasudin ka’idojin, CBN ya ce “Don samar da karin matakan da suka dace na kwastomomi ga cibiyoyin hada-hadar kudi a karkashin tsarin babban bankin Najeriya, don ci gaba da bin ka’idojin da suka dace na haramtattun kudade (Rigakafi da Hana). Dokar (MLPPA), 2022, Dokar Ta’addanci (Trevention and Prohibition) Act (TPPA), 2022, Babban Bankin Najeriya (Anti-Money Laundering, Combating the Financing of Terrorism and Countering Proliferation Financing of Weapon of Mass Destruction in Financial Institutions) Dokokin, 2022 (CBN AML, CFT da Dokokin CPF) da mafi kyawun ayyuka na duniya.
“Kuma ba da damar CBN ta aiwatar da bin ka’idodin kwastomomi daidai da ka’idojin CBN AML, CFT da CPF.”
Babban Bankin ya kara da cewa, cibiyoyin hada-hadar kudi ba za su kafa ko ajiye asusu ba, ko asusu masu lamba, ko asusu da sunan karya.


