Babban bankin ƙasa CBN, ya bai wa bankunan kasuwanci izinin yin musayar kudaden waje ta kowane farashi.
Izinin yana nufin cewa yanzu bankuna suna da ikon sayar da dala a ƙayyadaddun ƙimar kasuwa.
DAILY POST ta tattaro cewa wasu bankunan sun sanya darajar dalar Amurka zuwa Naira a kan N699 zuwa N750, lamarin da ke nuni da cewa a yanzu Najeriya na gudanar da canjin cikin ‘yanci daidai da alkawarin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi na farfaɗo da darajar Naira.
Da yake mayar da martani game da ci gaban a wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Laraba, Dr. Andrew Nevin, Masanin Tattalin Arziki, ya ce hadewar farashin kudaden waje zai yi tasiri sosai a kasar ta hanyar bunkasa damar saka hannun jari a Najeriya.
“Abin da ke faruwa shi ne, CBN yana karbar daloli daga asusun tarayya yana baiwa masu hannu da shuni akan Naira 411 zuwa Dalar Amurka yayin da farashin dala ya kai N700 zuwa N750, a gaskiya ba mu sani ba saboda sun cire gaskiya.
“Abin da ya faru shi ne gwamnatin jihohi ba za ta iya biyan ‘yan fanshonsu ba. Wannan muhimmin al’amari za a magance shi ta hanyar ci gaba. Yanzu gwamnatin jihar za ta samu cikakken darajar dalar ta.
“Zai yi matukar tasiri a tsarin kasafin kudin kasar nan idan muka daina baiwa masu hannu da shuni dala. Muna samun ingantacciyar saka hannun jari, da yin amfani da albarkatun kasa na adalci da inganta yanayin kasuwanci, hakan zai karfafa kudin Najeriya,” inji shi.
Shekaru da dama, Najeriya ta ci gaba da sarrafa farashin musaya a hukumance yayin da kudaden da ake samu na kudin waje ya samu koma baya. Yayin da CBN ya ci gaba da samun kudin wucin gadi na $1/N462.


