fidelitybank

CBN ta magantu a kan karanci kudi da ake fama da shi

Date:

Babban bankin Najeriya, CBN, ya ce isassun takardun kudi na Naira na yaduwa a yayin da ake samun rahotannin karancin kudaden.

A cikin wata sanarwa da Sashen Sadarwa na Kamfanin na CBN ya fitar, babban bankin ya bayyana dalilan da suka janyo karancin kudin Naira a wasu sassan kasar nan.

Matakin na CBN ya biyo bayan korafe-korafe da wasu abokan huldar bankuna ke yi kan karancin kudin da ake samu na Naira a kananun bankuna, Automated Teller Machines (ATMs), Points of Sale (PoS), da Bureaux de Change (BDCs).

Sai dai babban bankin ya ce ana ganin ana fama da karancin kudin ne sakamakon yadda bankunan Deposit Money Banks (DMBs) ke cire kudade daga rassa daban-daban na CBN.

Ya bayyana cewa janye firgici da abokan cinikin banki ke yi shi ma wani bangare ne ya haddasa karancin.

Babban bankin na CBN ya ce babu karancin kudin Naira, yana mai cewa akwai wadatattun kudaden a tattalin arzikin kasar.

“An jawo hankalin CBN akan rahotannin da ake zargin ana fama da karancin kudi a bankuna, ATMs, PoS da BDC a wasu manyan biranen kasar nan.

“Binciken da muka yi ya nuna cewa ana ganin karancin kudi a wasu wuraren ya samo asali ne saboda yawan cire kudi daga rassan CBN da DMBs suka yi da kuma firgita da kwastomomin da ke cirewa daga na’urar ATM.

“Yayin da muke lura da damuwar ‘yan Najeriya game da samar da tsabar kudi don hada-hadar kudi, muna so mu tabbatar wa jama’a cewa akwai isassun takardun kudi na ayyukan tattalin arziki a kasar,” in ji sanarwar.

vgn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp