fidelitybank

CBN na kan bakarta ba cire kudi a ATM – Emefiele

Date:

Babban bankin kasa, ya ce, babu gudu ba ja da baya a kan sabon tsarinsa na takaitawa ɗaidaikun mutane cire kudi daga bankuna bayan kiraye-kiraye daga ko’ina a Najeriya cewar ya sake duba batun.

Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ne ya bayyanawa manema labarai hakan a jiya Alhamis bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce batun da bankin zai sake dubawa shine adadin kudin da za a iya cirewa ba wai ya canja tsarin ba, inda ya ce sabon tsarin na nan daram.

Gwamnan babban bankin na magana ne bayan da majalisar wakilai ta nemi da a soke tsarin da kuma gayyatarsa zuwa gabanta domin ya yi mata bayani.

“Ina sane da batun jin karin bayani da ‘yan majalisa suka nema. Amma ina ganin abu mafi muhimmanci shi ne cewa tsarin ya faro ne tun a shekara ta 2012,” in ji Emefiele.

“Sai dai kusan sau uku zuwa hudu muna soke tsarin saboda muna ganin ya kamata mu yi kyakkyawan shiri da sake gyara tsarin biyan kudi a Najeriya.

”Tsakanin 2012 zuwa 2022, kusan shekara goma kenan, muna da yakinin cewa an samar da cibiyoyi na taimakawa mutane da dama yin hada-hadar kudaɗe a fadin kasa.

Emefiele ya ce akwai tsari da za a yi wa al’ummomi a karkara don tabbatar da cewa sabbin tsare-tsare ba su yi mummunan tasiri a kansu ba.

A ranar Talata ne, CBN ya taƙaita yawan kuɗade laƙadan da ƴan ƙasar za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki, inda yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.

ng news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp