fidelitybank

CBN bai ba mu isashshen kudi ba – Bankunan Kasuwanci

Date:

Bankunan kasuwanci sun mayar da martani kan iƙirarin babban bankin kasa CBN kan cewa, ya bai wa bankunan kasuwanci isassun sababbin kuɗaɗe kawai sun riƙe su ne.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, Mrs Hadiza Ambursa wadda jami’a ce a Access Bank, wadda ta wakilci manajan darakta ta ce, an ba su kashi 10 ne kacal cikin 100 na kuɗin da suka bai wa CBN.

A yayin wani zama da wakilan bankunan kasuwanci suka yi da kwamitin majalisar Najeriya, ma’aikaciyar ta ce “Ba ma samun kuɗin cikin gaggawa kamar yadda muke buƙata. Muna samun kashi 10 ne kawai cikin 100 na abin da muka kai wa CBN. Muna biya muna kuma karɓa kudi. Kuma a gefe ɗaya muna sanya kuɗin a ATM.

Mista Jimoh Garuba wanda wakilin Sterling Bank ne, yana samun kuɗi daga CBN amma ba ya kai wa yadda zai isa ga buƙatun kwastomominsa.

Yace, bankinsu na karɓar abin da bai gaza naira miliyan 150 ba daga CBN kowanne mako su rabawa reshinansu da ke Abuja.

Ya ƙara da cewa a Kaduna, bankinsu ya ƙarbi naira miliyan 150 a kowanne mako ya kuma raba su ga duka rassansa da ke jihohi 36 na tarayya.

Ya ce a Kano, “ana bamu naira miliyan 100 ne a mako, ba za mu iya komau da su ba bayan sanyawa a na’urar ATM”.

Ms Arerepade Akagwe, wadda wakilin United Bank for Africa (UBA) ne, ta ce ta karbi kashi 70 na tsofaffin kuɗin da ta bai wa CBN.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN akwai sauran bankuna irinsu Guarantee Trust Bank (GTB), ECO bank, Lotus Bank da Fidelity da suka amince sun karɓi kimanin kashi 60 na tsafaffin kuɗin da suka mayar wa CBN.

Shugaban kwamitin ɗan majalisar wakilai alhassan Ado-Doguwa ya ce gayyatar da aka yi wa bankunan ba abin ta da jijiyar wuya ba ne, yanayi ne na bincike kan abin da ya shafi al’umar Najeriya.

“Muna da buƙatar sanin gaskiya kan ainihin iƙirarin da bankunan kasuwanci suke yi na cewa CBN bai bayar da sabbin kuɗi ba, da kuma na CBN da ke cewa ya bayar da kudaden da suka kamata.

vanguard newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...
X whatsapp