Hukumar kwallon ƙafa ta Afrika CAF ta sanar da cewa ta samu bayanai kan abin da yake faruwa tsakanin hukumomin kwallon kafa na Najeria da Libya a wasan neman gurbin shiga gasar kofin ƙasashen nahiyar ta 2025.
CAF ta ce ta tuntuɓi hukumomin kwallon kafar ƙasashen Najeriya da na Libya domin jin abin da yake faruwa game da yadda tawagar Super Eagles ta maƙale a filin jirgin sama da ke Libya awanni masu yawa, bayan nan aka ce su sauka.
A yanzu dai Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika ta gabatar da wannan matsala ga kwamitin ladabtarwarta domin bincike tare da ɗaukar mataki kan wanda ya karya dokar hukumar.
Tuni dai ƴan wasan Super Eagles suka kama hanyar komawa gida Najeriya, bayan Super Eagles ta yi zargin cewa da gangan hukumomin Libya suka sauya filin jirgin da ya kamata su sauka, yayin da ita ma hukumar ƙwallon Libya ke cewa sun fuskanci irin wannan matsalar lokacin da suka je Najeriya.