Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika CAF ta sake bude gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2025.
Da farko dai an baiwa Guinea damar karbar bakuncin gasar amma a hukumance CAF ta kwace wa kasar da ke yammacin Afirka ‘yancin a karshen makon da ya gabata.
CAF ta dauki matakin ne bayan Guinea daya daga cikin kasashe mafi talauci a nahiyar, ta bayyana a hukumance cewa ba ta shirya karbar bakuncin gasar ba.
Shugaban CAF, Patrice Motsepe da babban sakatare, Veron Moshengo-Omba sun gana da shugaban rikon kwarya na Guinea, Kanar Mamady Doumbouya a karshen mako.
Rashin gazawar Guinea ya samo asali ne saboda ababen more rayuwa da kayan aikinta da ba su shirya karbar bakuncin gasar ta kungiyoyi 24 ba.
Cote d’voire za ta karbi bakuncin gasar AFCON na gaba a shekarar 2023.