Burtaniya ta sanar da saka jerin takunkumi kan wasu manyan sojojin ƙasar Iran da ƙungiyoyi sakamakon harin da Iran ɗin ta kai wa Isra’ila ranar 1 ga watan Okotoba.
Mutanen da takunkumin ya shafa sun haɗa da Abdol Rahim Mousavi, wanda kwamanda ne na sojojin Iran sannan kuma mamba na majalisar ƙoli ta tsaro ta Iran da kuma Hamid Vahedi wanda shi kuma kwamanda a rundunar sojin saman na Iran.
Mutanen da aka sanyawa takunkuman za su fuskanci haramci tafiye-tafiye da kuma hana su amfani da kuɗaɗensu, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Burtaniyar ta sanar.
Hukumar kula da sararin samaniyyar ƙasar Iran wadda ke ƙera fasahohin da ake amfani wajen ƙera makamai masu linzami da ke gudun ƙifta ido, ita ma takunkumin ya shafe ta ta hanyar hana ta amfani da kuɗaɗ da kadarori. In ji BBC.
A ranar 1 ga watan oktoba ne dai Iran ɗin ta ƙaddamar da hari a kan Isra’ila inda ta aike da makamai masu linzami masu gudun kiftawa da Bisimilla fiye da 180.
Sojojin Isra’ila sun ce sun kama mafi yawan makaman.