Burkina Faso ta kori jami’an diflomasiyya uku saboda neman tayar da ƙayar baya, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta shaida cikin sanarwar da ta aike wa Faransa.
Sanarwar na ɗauke da kwanan watan 16 ga watan Afrilu sai dai ba ta yi cikakken bayani kan ayyukan da jami’an suka yi ba.
An buƙaci jami’an diflomasiyyar da suka haɗa da mashawarta kan harkokin siyasa biyu a ofishin jakadancin Faransa a Ouagadougou, su fice daga Burkina Faso cikin sa’a 48,” in ji sanarwar.
Alaƙa tsakanin Burkina Faso da Faransa – ƙasar da ta mulke ta a baya ta yi tsami tun da Kyaftin Ibrahim Traore ya ƙwace mulki a juyin mulkin da aka yi a Satumbar 2022.
Shugaban sojin da ke mulki ya karkatar da alaƙar Burkina Faso ga Rasha tare da kawo ƙarshen kusancinsu da Faransa.
A ƙarƙashin mulkinsa, an kori jami’an diflomasiyyar Faransa da dama kuma an rufe sansanin sojojin Faransa da ke ƙasar.