Gwamnatocin soji a ƙasashen Nijar, da Burkina Faso, da Mali sun bayar da shawarar kafa ƙasa ta tarayya da za ta haɗa ƙasashen uku na Afirka ta Yamma kuma maƙwabtan juna.
Sun bayyana shawarar ce bayan ganawar da ministocin harkokin wajensu suka yi a birnin Bamako na Mali a ƙarshen makon nan.
Lamarin na zuwa ne yayin da Nijar da Burkina Faso ke son bin sawun Mali na ficewa daga ƙungiyar ƙasashen G5, wadda aka kafa don yaƙar masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.
Wata sanarwar bayan taron ministocin ta ce ƙasashen sun bayyana “babban yunƙurinsu na zaman lafiya, da cigaba, da kuma difilomasiyya” da kafa ƙasar zai samar.
“Ministocin…da ke da burin haɗe Burkina Faso, da Mali, da Nijar sun bai wa shugabannin ƙasashen shawarar kafa ƙasa ta tarayya mai suna Alliance of Sahel States,” a cewar sanarwar. Alliance of Sahel States na nufin Ƙasashen Ƙawance na Sahel.
Ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma Ecowas ta dakatar da ƙasashen uku daga cikinta bayan sojoji sun hamɓarar da gwamnatocin farar hula a ƙasashensu


