Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya ce, matakan da shugaban ƙasa Bola Tinubu yake ɗauka wajen inganta tattalin arzikin Najeriya na nuna yadda shugaban ya damu da damuwar ƴan ƙasar.
Abbas ya bayyana haka ne a jawabinsa a lokacin da shugaban ƙasa Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024 a gabatan majalisar dokokin ƙasar a ranar Laraba.
A cewarsa, “majalisar dokoki za ta ci gaba da goyon bayan matakan gyare-gyaren da kake ɗauka ta hanyar yin dokoki da kuma tattaunawa tare da wayar da kan mutane domin ƙarin fahimta da amincewa
Abbas ya ƙara da cewa tafiye-tafiyen da shugaban yake yi sun ƙara ɗaga darajar ƙasar a idon duniya.
Sai dai ya ce akwai buƙatar a yaba da sadaukawar da ƴan Najeriya suka nuna, inda ya ce cire tallafin man fetur da hauhawar farashin kayayyaki da wasu matakan inganta tattalin arziki sun haifar da ƙalubale sosai
“Sai dai ana buƙatar irin wannan sadaukarwar domin ƙasa ta ci gaba.”