Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya jaddada kudirinsa na sake bude dukkan iyakokin kasashen duniya tare da karfafa tsaron kasa idan har aka zabe shi a matsayin shugaban kasar.
Atiku ya bayyana haka ne a jiya a lokacin da yake jawabi ga dimbin jama’a a wani taron gangamin shugaban kasa da aka gudanar a Damaturu, jihar Yobe.
Dan takarar shugaban kasar ya ce manufarsa ta sake bude iyakokin, ita ce kasuwanci tsakanin Najeriya da makwabtanta.
Atiku ya tambayi jama’ar, “Kuna son zaman lafiya ya dawo Yobe? Suka amsa cikin mawaƙa “Eh”.
Daga nan ya ba su tabbacin cewa idan suka zabi PDP a zabe mai zuwa zaman lafiya zai dawo Yobe.
Karanta Wannan: Wike ya amince Atiku ya gudanar da ayakin zabensa
“Za mu tabbatar da cewa makarantunmu a bude suke domin ‘ya’yanmu su ci gaba da zuwa makarantu.
“Mun kuma yi alkawarin ba wa matasanmu maza da mata karfin gwiwa ta hanyar ba su jari don kafa sana’o’i domin samun nasarar rayuwa,” Atiku ya tabbatar.
Domin samun sauyi mai ma’ana, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya bukaci masu zabe a jihar da su fito baki daya su zabi PDP.
A wajen gangamin yakin neman zaben shugaban kasa, shugabannin jam’iyyar na kasa sun karbi bakuncin magoya bayan jam’iyyar APC sama da 460 da suka sauya sheka zuwa PDP a hukumance tare da mika tuta ga dan takarar gwamnan jam’iyyar a jihar Yobe, Shariff Abdullahi.