Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya ce, ya himmatu wajen inganta rayuwar ma’aikatan ƙasar ta hanyar ba su albashi mai kyau da kuma inganta wuraren ayyukansu.
Shugaban na wannan magana ne yayin da yake tattaunawa da haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC da kuma ta ‘yankasuwa TUC a fadarsa a yammacin Alhamis.
“Ina sane da duk abubuwan da ke faruwa a kusa da ni,” a cewarsa. “Ma’aikacin da ke cikin farin ciki shi ne mai himma, kuma al’umma ta dogara ne kan ma’aikacin da ke cikin walwala.”
Sai dai kuma ya nemi ‘yanƙasa su rage buri game da sabon mafi ƙanƙantar albashin, wanda gwamnati da ‘yan ƙwadagon ke tattaunawa a kai.
“Dole ne a yi abu daidai ruwa daidai tsaki. Kafin mu daddale kan mafi ƙanƙantar albashi dole ne mu duba tsarin. Me ya sa za mu dinga ƙara albashi duk shekara biyar? Me ya sa ba shekara biyu ko uku ba? Wace matsala muke da ita a yau? Ko za mu iya magance ta gobe?”
Bayan kammala tattaunawar, Shugaban NLC Joe Ajaero ya ce kowa yana nan kan bakarsa a yanzu; gwamnati na tayin N62,000, su kuma suna neman N250,000. Amma za su sake zama da gwamnatin a mako mai zuwa.


