Gwamnan Yobe Mai Mala Buni, ya bai wa ma’aikata hutun kwanaki biyu wato Litinin da Talata domin ziyarar da shugaba Buhari zai kai jihar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar dauke da sa hannun shugaban ma’aikata na jihar, Alhaji Garba Bilal a Damaturu a ranar Lahadi.
Buhari zai ziyarci jihar domin kaddamar da wasu manyan ayyuka ciki har da tashar jirgin sama ta sauke kaya da wani katafaren kasuwar zamani da kuma cibiyar lafiya.
Gwamnati ta ce ta bada hutu ne domin ma’aikata da sauran al’umma su samu damar tarbar shugaban wanda zai kai ziyarar kwana guda a jihar.
Sai a ranar Laraba ake sa ran ma’aikata su koma bakin aikinsu.