fidelitybank

Buhari zai taron gaggawa a kan matsalar da ake fuskanta

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari, zai jagoranci wani taron gaggawa na majalisar magabata a ranar Juma’a mai zuwa 10 ga watan nan na Fabrairu, ranar da aka sanya wa’adin daina amfani da wasu daga cikin manyan takardun kudi.

Taron zai tattauna ne a kan matsalolin da kasar ke fama da su a yanzu da suka hada da karancin man fetur da na kudin kasar Naira da matsalar tsaro yayin da kasar ke fuskantar babban zabenta da za a fara ranar 25 ga watan nan nan Fabrairu wato kasa da sati uku daga yanzu.

Karanta Wannan: Arewa ce ya kamata ta gaji Buhari – Dogara

Halin da kasar ke ciki na wadannan matsaloli musamman karancin Naira da kuma matsalar mai sun sa an fara zanga-zanga a wasu sassan kasar da dama.

Jaridar Daily Trustt ta ruwaito cewa, ana sa ran gwamnan Babban Bankin Najeriyar, Godwin Emefie zai yi wa majalisar bayani a yayin taron da zai gudana a fadar shugaban kasar, da ke Abuja, game da batun canjin kudin ksara, lamarin da ya jefa al’umma da dama cikin halin kaka-ni-kayi.

Haka kuma jaridar ta kara da cewa wasu kafofi na fadar shugaban sun gaya mata cewa shugaban hukumar zaben kasar, Farfesa Mahmood Yakubu, da shugaban ‘yan sanda na kasar Usman Alkali Baba za su yi wa majalisar bayani kan shirye-shiryen zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar tarayya da za a yi ranar 25 ga watan na Fabrairu da kuma na gwamnoni da ‘yan majalisar jiha da za a yi ranar 11 ga watan Maris.

Majalisar magabatan ta kunshi shugaban kasar da mataimakinsa da sakataren gwamnatin tarayya da tsofaffin shugabannin kasa da tsofaffin manyan alkalan kasa da shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai da gwamnonin jihohi 36 da kuma babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a.

legit nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp