A yau ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai tashi daga Abuja, domin halartar taron kungiyar ci gaban kasa da kasa (IDA) na kasashen Afirka a birnin Dakar na kasar Senegal.
Shugaban kasar zai samu rakiyar ministocin harkokin kasashen waje, Geoffery Onyeama; Kudi, Kasafi da Tsare-tsare na Kasa, Zainab Ahmed; da kuma Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo.
Sauran da ke cikin tawagar sun hada da: Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele; Darakta-Janar, Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Amb. Ahmed Rufa’i Abubakar; Darakta Janar, Ofishin Kula da Bashi, Patience Oniha; da kuma Manajan Daraktan Bankin Masana’antu, Olukayode Pitan.