fidelitybank

Buhari zai tafi Habasha taron ƙungiyar Tarayyar Afirka

Date:

Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin halartar taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) karo na 36, a yau Alhamis.

A wata sanarwa da kakakin shugaban, Mallam Garba Shehu, ya fitar, ya ce, a yayin da yake birnin na Addis Ababa, Buhari zai halarci wasu manyan taruka uku, a kan tsaro da zaman lafiya da batun sauyin yanayi da kuma yanayin siyasar da ake ciki a wasu ƙasashen yammacin Afirka.

Sanarwar wadda ta bayyana taken taron a matsayin, hanzarta aiwatar da tsarin kasuwanci maras shinge na nahiyar Afirka, ta kuma bayyana cewa, shugaban zai halarci wani taro na musamman na shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma da za a yi a gefen babban taron na AU.

Kakakin ya ce, taro na farko da za a yi shi ne na kwamitin tsaro na shugabannin ƙasashen ƙungiyar a kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Dumukuradiyyar Kongo, wanda shugaban Afirka ta Kudu zai jagoranta a matsayinsa na shugaban kwamitin a watan Fabarairu.

”Sai kuma taron kwamitin shugabannin ƙasashe da gwamnatoci a kan sauyin yanayi wanda shugaban Jamhuriar Nijar ke jagoranta,” in ji sanarwar

Shugaba Buharin wanda zai samu rakiyar wasu ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati zai koma Najeriya ranar Litinin 20 ga watan nan na Fabarairu, kamar yadda sanarwar ta ce.

today daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp