fidelitybank

Buhari zai rattaɓa hannu a kasafin kuɗi 2023 – Lawan

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2023 a ranar Talata mai zuwa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Juma’a, bayan wata ganawar sirri da ya yi da shugaban a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Lawan ya kuma bayyana cewa ya tattauna wasu batutuwan da suka shafi kasa da shugaban kasa, ciki har da tallafin da majalisa ke baiwa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) gabanin zaben 2023, da bukatar karin lamuni da Buhari ya nema da dai sauransu.

A cewar sa: “Muna sa ran shugaban kasa ya rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2023, da yardar Allah, ranar Talata.

“Wannan ya faru ne saboda mun rattaba hannu kan takardar a jiya, bayan da muka yi hasarar wani lokaci saboda wasu bata-gari da muka samu a cikin kudirin da aka gabatar wa Majalisar Dokoki ta kasa.

“Amma alhamdulillahi, NASS (Majalisar Tarayya) a majalisun biyu sun zartar da kasafin kudin shekarar 2023 a ranar Laraba.

“Kuma abu na farko a ranar Talata, na yi imanin cewa shugaban kasa zai rattaba hannu kan kasafin kudin 2023.”

latest news in nigeria today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Na so komawa Manchester United a 2012 – Lwandowski

Ɗanwasan gaban ƙungiyar Barcelona ta Spain, Robert Lewandowski ya...

Isak ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gaba Alexander Isak ya nace sai ya bar...

Sadiq Umar da Bello El-Rufai sun sayi ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna

Ɗanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya da Real Socieded...

Atiku zai iya guduwa daga ADC ya koma PDP idan Jonathan ya tsaya takara – Diran

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa,...

Zoben matar Ronaldo ya kai dala miliyan 5 – Masana

Masana sun yi kiyasin tsadar zoben da Cristiano Ronaldo...

Kama Tambuwal ya na da alaka da shigarsa cikin hadakar jam’iyya – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce kama...

Ambaliyar ruwa ta kashe mutuane takwas a Ebonyi

Ambaliya, wadda mamakon ruwan sama ya janyo, ta yi...

Bankin Duniya zai kashe wa yankin Arewa a Najeriya dala miliyan 300

Bankin Duniya ya amince da kasafin kuɗi dala miliyan...

Giyar mulki na kwasar Trump – ‘Yan Majalisar Democrat

'Yan Democrats a Amurka sun zargi Donald Trump da...

Kama Aminu Waziri Tambuwal da EFCC ta yi ba daidai ba ne – PDP

Jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da...

An kai hari a ƙauyuka 15 na Zamfara a mako ɗaya – Rahoto

Wani rahoto da tashar Channels ta ruwaito daga cibiyar Zamfara Circle...

Jihohin Arewa huɗu ne suke biyan mafi ƙarancin fansho na N32,000 – NUP

Ƙungiyar ƴan fansho na arewacin Najeriya, NUP ta ce...
X whatsapp