Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Landan, kasar Birtaniya, domin ganin Likitocinsa na tsawon makonni biyu, bayan halartar taron majalisar dinkin duniya da za ayi a Kenya.
Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.
Ya ce: “Shugaba Buhari zai tashi daga Abuja yau Talata 1 ga Maris don halartan murnar cika shirin majalisar dinkin duniya na yanayi shekaru 50 (UNEP@50), da aka shirya yi ranar 3-4 ga Maris, 2022, a Nairobi, Kenya, sakamakon gayyatar da takwararsa na Kenya, Uhuru Knyatta yayi masa.”
Adesina ya ce, shugaba Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama da Karamar ministar yanayi da Sharon Ikeazor da NSA Manjo Janar Babagana Monguno da DG na NIA, Ambasada Rufai Abubakar, da Shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.