Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai gabatar da kasafin kudi na shekarar 2023 a ranar Juma’a a gaban Majalisar Dokokin.
Shugaban zai gabatar da kasafin da yawansa ya kai Naira tiriliyan 19.76.
Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan a zaman majalisar na ranar Talata ya ce, za a gabatar da kasafin kudin ne da misalin ƙarfe 10 na safe a zauren majalisar wakilai.