Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai sake yin tafiya zuwa ƙasar waje kwana ɗaya bayan ya dawo daga ƙasar Sifaniya a nahiyar Turai ranar Juma’a.
Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban ƙasa Femi Adesina ya fitar a yau Asabar, ta ce, Buhari zai yi balaguron ne wannan karon zuwa Ghana, domin halartar taron Ecowas, ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma.
Taron na shugabannin ƙasashen Ecowas, zai duba halin da ake ciki a ƙasar Mali da kuma siyasar yankin Afirka ta Yamma baki ɗaya.
Buhari zai tafi Ghana a yau Asabar, inda zai koma Najeriya a yau ɗin bayan kammala taron.
Ƙasashen da tattaunawar za ta fi shafa sun haɗa da Burkina Faso da Mali da Guinea. In ji BBC.