Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai kuma ya nuna ɓacin ransa dangane da fille kan da ƴan IPOB suka yi wa wasu sojoji biyu da ke shirin aure.
An fille kawunan mutanen ne a karshen mako yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Imo, domin yin bikin aurensu na gargajiya.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu ya yi, Shugaba Buhari ya yi ta’aziyya ga rundunar sojoji da kuma iyalan Master Warrant Officer Audu Linus da kuma Private Gloria Mattew waɗanda ƴan IPOB suka fille kawunansu bayan sun harbe su.
Buhari ya nuna kaɗuwarsa kan wannan lamari inda ya alaƙanta wannan kisa da dabbanci, inda ya ce wannan aika-aika ta saɓa wa al’adu da zamantakewa.