Mai magana da yawun tsohon Shugaban Najeriya Muhammad Buhari, Mallam Garba Shehu, ya bayar da labarin yadda marigayin ya ƙi karɓar wasu kyautuka lokacin yana mulki, ciki har dakyautar jirgin sama.
Da yake magana ta cikin shirin Inside Sources na Channels TV, Garba Shehu ya ce Buhari ya ƙi amincewa da karɓar kyautar agogon lu’ulu’u wani ɗankasuwa a Najeriya ya ƙera da sunansa a jiki, da kuma kyautar jirgin sama da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta yi masa tayi.
“Shugaban ƙasa ya kalli agogon, ya ce ‘Agogon lu’ulu’u? Ba zan iya saka wannan ba. Ku faɗa masa yana ƙoƙari…kuma za mu ci gaba da ƙarfafa masa gwiwa. Ya ci gaba da ɗaukaka sunan Najeriya, amma ku mayar masa da agogon nan. Ba zan iya amfani da shi ba.’,” kamar yadda Garba ya bayyana ranar Juma’a.
Ya kuma bayar da labarin ziyarar da Buhari ya kai birnin Dubai a 2016, inda shugaban ƙasar ya yi masa tayin kyautar jirgin sama da zai yi amfani da shi har bayan ya sauka daga mulki, amma marigayin ya ƙi karɓa saboda ba gwamnatin Najeriya za a ba wa ba.
“Sarkin Abu Dhabi ya tambayi shugaban ƙasa [Buhari] wane nau’in jirgi ya fi so. Sai [Buhari] ya ce idan gwamnatin Najeriya za a ba wa zan karɓa. Sai sarkin ya ce a’a naka ne na ƙashin kai, ta yadda ko da ka bar mulki za ka ci gaba da amfani da shi.
“Buhari ya ce ba ni buƙatar jirgi idan na bar mulki, ba zan ma iya kula da shi ba,” in ji Garba Shehu.