Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres ya kai ziyarar ta’aziyya ofishin jakadancin Najeriya da ke birnin New York domin jajanta rasuwar marigayi Muhammadu Buhari.
Yayin ziyarar tasa a ranar Asabar, Mista Guterres ya sanya hannu kan rajistar masu ta’aziyya.
Ya bayyana hidimar da Buhari ya yi wa Najeriya da Afirka a matsayin abubuwan da za a dinga tunawa da si.
“A madadin MDD, ina miƙa ta’aziyyata game da rasuwar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari,” kamar yadda ya rubuta a rajistar.