Shugaba Muhammadu Buhari, ya yi Allah-wadai da jerin hare-haren da aka kai waɗanda suka yi sanadin kashe sama da mutum 150 a jihar Filato.
A martaninsa na farko bayan kashe-kashen na ranar Lahadi, Shugaba Buhari ya ce, ba za a taɓa yafe wa “masu wannan aika-aika ba” kuma “ba za su samu rahama ba”.
Ya dai bayyana lamarin a matsayin hare-haren ta’addanci.
Shugaban ya mika ta’aziyya ga iyalai da dangin mutanen da hare-haren suka shafa.