Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Tajudeen Abba ya miƙa ta’aziyyar mutuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yana mai siffanta da “mutumin da ba shi aikata cin hanci”.
Tajudeen ya ce Buhari ya yi rayuwa “mai sauƙi maras ƙyale-ƙyale, mai wadatar zuci wadda kuma ta sama masa girmamawa da amincewa a faɗin ƙasa”.
Buhari ya rasu yau Lahadi a birnin Landan bayan fama da jinya.
Gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda ya ce za a yi jana’izarsa a garin Daura mahaifarsa.