Shugaba Muhammadu Buhari, ya jajantawa Sanata Kabiru Gaya, mai wakiltar Kano ta Kudu, bisa mutuwar dansa Sadiq a wani yanayi mai sarkakiya kwanakin da suka gabata.
A sanarwar da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar yau Laraba, inda ya ce, Shugaban na jajantawa iyalan Sanata Gaya, bisa wannan mummunan al’amari da ya same su.
Ya kuma ce, yana fatan binciken yan sanda zai bankado gaskiyar yadda lamarin ya faru, da kuma kama masu hannu a kisan nasa da ake zargi.
Ana zargin cewa, kashe Sadiq Kabiru Gaya aka yi a Abuja mako daya da wucewa, kuma rahotanni sun ce, tuni yan sanda sun kama mutum biyar da suke zargi da hannu a kisan, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.


