Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis a Lafia, Jihar Nasarawa, ya ce, ya yi rantsuwa da Kur’ani mai tsarki cewa, wa’adi biyu kawai zai yi a ofis.
The Punch ta rawaito cewa, Buhari ya kuma ce, ya kamata shugabanni da ke yin rantsuwar kama aiki da littafai masu tsarki su yi takatsantsan da jagorancin da Allah da al’umma suka basu.
Buhari, wanda ya kai ziyarar aiki ta kwana biyu a Nasarawa, ya yi wannan furucin ne a fadar Sarkin Lafia, Sidi Muhammad I, inda ya jadada cewa ba zai wuce wa’adi biyu da kundin tsarin mulki ta kayyade ba.