Shugaban kasa, Muhammadu Buhari. ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa masu ibada a wata cocin katolika ta St Francis a garin Owo a jihar Ondo.
Shugaban ya ce, maƙiya ne kawai za su aikata wannan mummunan aikin, yana mai cewa za su fuskanci baƙin cikin duniya da na lahira.
Shugaba Buhari ya jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe da cocin Katolika da gwamnatin jihar Ondo, inda ya buƙaci hukumomin agajin gaggawa su kai ɗauki ga waɗanda suka jikkata.
Ƴan bindigar sun abka cocin ne a ranar Lahadi, mutane na tsakar ibada suka buɗe masu wuta. Bayanai sun ce an kashe mutane da dama tare da sace wasu da ba a san adadinsu ba.