fidelitybank

Buhari ya yi ƙarin ladan tafiye-tafiye na DTA ga ma’aikatan gwamnati

Date:

 

 

 

Gwamnatin Taraiya ta amince da ƙarin kuɗin tafiye-tafiye da a ke baiwa maikata, wanda a turance a ke kira da Duty Tour Allocation, DTA.

Shugaban Hukumar kula da Albashi da Haƙƙoƙin Ma’aikata ta Ƙasa, Ekpo Nta ne ya baiyana hakan ga manema labarai a Abuja a jiya Alhamis.

Mata ya ce sabon ƙarin ladan tafiye-tafiyen zai fara aiki ne da ga 1 ga watan Fabrairu, inda ya baiyana farin ciki game da ci gaban da a ka samu.

“Wannan wani tagomashi ne ga ma’aikata. Gwamnatin Taraiya na ƙoƙarin kyautata walwalar ma’aikata.

“Ma’aikata da ke matakin albashi na 01 zuwa 01 yanzu za su riƙa karɓar N10,000, daga mataki na 05 zuwa 06 kuma N15,000, su kuma na mataki 07 zuwa 10 za su riƙa karɓar N17,500.

“Haka kuma masu matakin albashi na 12 zuwa 13 za su riƙa karɓar N20,000, na matakin 14 zuwa 15 kuma za su samu N25,000, inda mataki na 16 zuwa 17 za su riƙa karɓar N37,000,” in ji shi.

Nta ya tuna cewa, a baya, DTA ɗin ma’aikaci mai matakin albashi na 06 zuwa ƙasa N5,000 ne, yayin da na mataki 07 zuwa 14 N12,000 ne, sannan na matakin albashi 15 zuwa 17 N16,000 ne.

Ya yabawa Gwamnatin Taraiya da a kullum ta ke kula da walwalar ma’aikatan ta.

Shugaban ya kuma yabawa kafafen yaɗa labarai a bisa ƙoƙarin su na ilmantar da al’umma, inda ya hore su da su ɗore da kyawawan aiyukan da su ke yi

nnn.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An kashe kwamandan Boko Haram a tafkin Chadi

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun sanar da kisan wani jagoran...

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...
X whatsapp