Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da sabon shugaban hukumar tattara kudaden shiga da kasafi (RMAFC), Mohammed Shehu.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), ya ruwaito cewa, an gudanar da rantsar da shugaban ne jim kadan gabanin fara taron tattaunawa na mako-mako na majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a ranar Laraba a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
NAN ta ruwaito cewa, nadin Bello ya biyo bayan murabus din tsohon shugaban hukumar, Elias Mbam, wanda ya fafata a zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Abia.
Da yake zantawa da manema labarai na fadar gwamnati, Bello ya yi alkawarin yin aiki tukuru don taimakawa kasar nan ta samu karin kudaden shiga a cikin dokokin da suka wuce.


