Shugaba Muhammadu Buhari, ya taya Patricia Scotland murnar sake zaɓarta a matsayin babbar sakatariyar ƙungiyar rainon ƙasashen Ingila.
Shugaban ya taya ta murnar ne a shafinsa na Twitter inda ya yi mata addu’ar gudanar da aikinta lafiya.
Shugaban ya kuma jinjina mata da irin aikin da ta yi a tsawon shekara shida na jagorancin ƙungiyar kuma ya yaba mata da irin goyon bayan da ta rinƙa ba Najeriya.