Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Biodun Oyebanji murnar lashe zaben gwamnan jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar.
Shugaban ya ce, wannan nasara ta dace sosai idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da Oyebanji ya bayar wajen ci gaban jihar da kuma jam’iyyar kafin a zabe shi a matsayin mai rike da madafun iko, inda ya bukace shi da ya yi fice wajen samun nasara domin amfanin al’ummar jihar.
Shugaba Buhari ya kuma yi murna da shugaban jam’iyyar APC, Sanata Abdulahi Adamu, da kwamitin ayyuka na kasa, bisa nasarar da aka samu, na farko a karkashin sabbin zababbun shugabannin jam’iyyar.