Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya mika sakon taya murna ga asalin ‘yan kasar mazauna Amurka su takwas da suka samu nasarar lashe kujeru daban-daban a zaben rabin wa’adi da aka gudanar a kasar.
A jihar Georgia mutum biyar ne ‘yan asalin Najeriya suka lashe kujerun majalisar dokokin jihar a gundumomin da suke zaune.
Sannan kuma mutum guda-guda ya ci kujerun majalisa a jihohin Pennsylvania da Minnesota.
Haka kuma an sake zabar Dakta Oye Owolewa a kujerar majalisar wakilan kasar daga birnin Washington D.C
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan kafofin yada labarai mista Femi Adesina ya fitar, Shugaba Buhari ya yi musu fatan alkairi a tsawon lokacin mulkinsu.
Sannan kuma shugaban ya gode musu bisa taimakekeniya da hadin kai da suke nuna wa junansu a tsawon shekarun da suka kwashe a Amurka.


