Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba da gudunmowar da kungiyar ‘yan Najeriya mazauna ketare ke bayarwa wajen daga martabar kasar a kasashen waje, bayan da aka zabi wani dan kasar mai suna Ayo Owodunni a matsayin bakar fata na farko da ya zama kansila a mazabar Kitchener da ke birnin London Ontario na kasar Canada.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba shehu ya fitar, shugaba Buhari ya ce nasarar da mista Owodunni ya samu a wannan zabe mai cike da tarihi, ya nuna karara yadda mutumin yake bullo da tsare-tsare na ci gaba, da goyon bayan ‘yan Najeriya mazauna Canada a matsayinsa na mai bayar da shawara da kuma kokarinsa na hada kan ‘yan kasar a kasar da yake zaune ta Canada.
Shugaba Buhari ya umarci ‘yan kasar mazauna ketare da su kasance jakadun gwamnatin kasar na gari a duk inda suka samu kansu a fadin duniya, ya kuma shawarce su da kada su ji shakkun cimma muradunsu”.
Daga karshe shugaban ya taya mista Owodunni tare da matarsa Folake da kuma yaransu biyu murnar nasarar lashe zaben, wanda ya bayyana a matsayin ”mai matukar muhimmanci’.