Shugabankasa, Muhammadu Buhari, ya taya Yarima Mohammed Bin Salman, mai jiran gadon sarautar Saudiyya, murnar zama firaiministan kasar.
Shugaban ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana d yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Laraba.
“Shugaba Buhari ya ce gwamnati da al’ummar Najeriya suna sa ran kara aiki tare da shi domin kyautata dangantakar da ke tsakaninsu,” in ji sanarwar.
Kazalika shugaban Najeriya ya yi addu’a ga Sarki Salman Bin Abdulaziz domin samun karin lafiya.