Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya karɓi baƙwancin jagoran gwamnatin Chadi Janar Mahamat Idiss Derby a Abuja yau Juma’a.
Ziyarar da ya kai Abuja jim kaɗan, bayan ya hau mulki, Shugaba Buhari ya tabbatar wa shugaban wanda ɗan tsohon Shugaba Idriss Deby ne cewa, Najeriya za ta taimaka wa ƙasarsa iya bakin ƙoƙarinta wajen komawa kan mulkin dimokuraɗiyya.
Ko da ya ke fadar shugaban ba ta yi ƙarin bayani kan abin da shugabannin biyu suka tattauna ba, Najeriya da Chadi na fuskantar hare-haren ‘yan Boko Haram.
Haka nan, Buhari ya gana da jakadan Qatar a Najeriya, Dr Ali Bin Ghanem Al-Hajri.