fidelitybank

Buhari ya taka rawar gani yanzu kuma Tinubu zai ɗora – Sakataren APC a ƙetare

Date:

Sakataren, APC a zaɓen 2023 dake ƙetare, Hon. Ifeoma Nwankwo wadda aka fi sani da Iyabo a yau ta ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka rawar gani a Najeriya.

Ta kuma jaddada cewa, ya samu nasarori masu kyau kuma ya yi iya kokarinsa ga Najeriya.

Hon. Nwankwo ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, a Chatham House dake birnin Landan.

A cewar Nwankwo, “Gwamnati tana ci gaba. Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai kaunarmu ya samu nasarori masu kyau kuma ya yi iya kokarinsa ga Najeriya.

“Mun yi imanin cewa shugaban kasa mai jiran gado, Tinubu zai karfafa tare da aiwatar da kyawawan manufofinsa don ci gaban kasa da ci gaban kasar.”

Ta bukaci ‘yan Najeriya da su zabi Tinubu da abokin takararsa, Alhaji Kashim Shettima, a zaben 2023 mai zuwa a kasar.

Ta ce Allah Madaukakin Sarki ya nada Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ta Alhaji Kashim Shettima shugabancin kasa a 2023.

Hon. Nwakwo, wanda ke da zama a Burtaniya, ya kuma ce ‘yan Najeriya da Najeriya za su amfana sosai daga Tinubu da Shettima domin dukkansu sun nuna iya shugabanci.

Ta yi nuni da cewa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje suna da cikakken amana da amincewa ga Tinubu da Shettima domin samar da mafita ga kalubalen da ake fuskanta a kasar.

latest news in nigeria 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp